Asabar 22 Agusta 2026 - 14:09
9 ga Rabi’ul Awwal: Ranar Sabunta Mubaya’a da Wazifar Mai Jiran Imam na Zamani

Hauza/ Masanin Mahdawiyya ya bayyana cewa ranar 9 ga Rabi’ul Awwal wata dama ce ga mabiya Ahlul-Baiti (A.S) ta sake duba dangantakarsu da Imamin Zamani(A.F), tare da sabunta mubaya’a da ƙarfafa ƙudurin yin biyayya, ɗaukar nauyi da kuma shirya al’umma domin bayyanarsa.

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Reza Nasouri, masani kan Mahdawiyya, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza kan ma’anar ranar 9 ga Rabi’ul Awwal, mubaya’a ga Imam a zamanin gaiba da kuma dangantakar Ashura da Mahdawiyya.

Ya ce farkon watan Rabi’ul Awwal yana da muhimmiyar ma’ana ga ‘yan Shi’a, saboda yana tunasar da shahadar Imam Hassan Askari (A.S) da kuma fara Imamancin Hazrat Waliyyul-Asr (A.F).

Ya bayyana cewa babu ingantacciyar hujja bayyananniya da za ta tabbatar da cewa ranar 9 ga Rabi’ul Awwal “Idi” ce ta musamman. Sai dai, saboda ranar 8 ga watan ita ce ranar shahadar Imam Hasan Askari (A.S), ranar 9 ga Rabi’ul Awwal ta zama wata dama ta sabunta mubaya’a ga Imamin Zamani(A.F).

A cewarsa, al’adar mabiya Ahlul-Baiti (A.S) ita ce, bayan shahadar wani Imam, su gabatar da ta’aziyya ga Imam da ya zo bayansa tare da sabunta mubaya’a gare shi. Saboda haka, ya dace a wannan lokaci mutum ya sake duba alkawarinsa da Imamin Zamani, ya auna yadda ya kasance mai aminci gare shi, sannan ya sabunta wannan alkawari.

Masanin ya jaddada cewa mubaya’a ba magana ce kawai ba, illa tana ɗauke da wasu nauye-nauye da mutum ya wajaba ya tsaya a kansu. Ya ce kafin mutum ya yi mubaya’a, ya kamata ya san abin da Imamin Zamani yake tsammani daga gare shi, sannan ya tsara rayuwarsa bisa wannan fahimta.

Ya bayyana cewa karɓar wilaya na nufin mutum ya daidaita rayuwarsa, halayensa, tunaninsa da shawarwarinsa da abin da Imam yake so da kuma yardarsa. Amma a zamanin gaiba, wannan nauyi yana bayyana ne ta hanyar jira (Intizar).

A cewarsa, jira ba zama ba ne, rashin aiki ko kallon abin da ke faruwa kawai ba; jira yana nufin aiki, shiri, gwagwarmaya da ƙoƙarin taimakon Imam.

Ya yi nuni da cewa Addu’ar Ahd tana ɗauke da muhimman bayanai kan irin nauyin da ke kan mai jiran Imam. Daga cikin abin da ake roƙa a cikinta akwai: “Ya Allah, Ka sanya ni cikin mataimakansa da masu taimakonsa.”

Ya ce wannan addu’a tana koyar da mai jira ya gina kansa har ya kai matsayin mutumin da zai iya taimakon Imam a aikace. Saboda haka, ya kamata ya san siffofin mataimakan Imam, sannan ya tsara tarbiyyarsa, salon rayuwarsa, tunaninsa da halayensa bisa waɗannan siffofi.

Hujjatul Islam Nasouri ya ƙara da cewa mai jiran Imam na gaskiya ya kamata ya kasance mai kare Imam da manufofinsa daga shubuhohi, tare da amfani da lokacinsa, dukiyarsa, ƙarfinsa da sauran damar da Allah Ya ba shi wajen taimakon tafarkin Imam.

Ya ce wannan taimako ba ya takaita ga ayyukan zamantakewa kawai, domin yana kuma haɗawa da gwagwarmayar mutum da kansa, sarrafa sha’awoyinsa, nisantar zunubi da kuma amfani da damar da yake da ita wajen gyaran al’umma.

Ya kuma bayyana cewa mai jiran Imam yana buƙatar kasancewa cikin masu ɗaukar mataki da wuri wajen cimma manufofin Imam, yana mai cewa samar da yanayin da zai taimaka wajen bayyanar Imam yana buƙatar gina mutane masu ƙwarewa, haɗa kan al’umma da tarbiyyar ƙwararrun mutane.

A cewarsa, ɗaya daga cikin muhimman manufofin Imamin Zamani shi ne kafa tauhidi, yaɗa ruhaniya da tabbatar da adalci a cikin al’umma. Saboda haka, zamanin gaiba ya kamata ya zama filin horo da kuma shirye-shiryen cimma waɗannan manufofi.

Masanin ya raba alkawarin mai jiran Imam zuwa fannoni daban-daban, ciki har da alkawarin sani da fahimta, alkawarin ɗabi’a da aiki, alkawarin zuciya da kuma alkawarin biyayya.

Ya ce wajibi ne mai jira ya ƙara sanin Imam da manufofinsa, ya gyara salon rayuwarsa domin ya dace da yardar Imam, sannan ya ƙarfafa ƙaunarsa da marmarin bayyanarsa.

Dangane da biyayya, ya ce mutum ya kamata ya koyar da kansa bin umarnin addini da kuma malaman addini na kwarai da Waliyyul Faƙih a zamanin ɓoye, domin ya kasance cikin shiri wajen biyayya ga Imamin Zamani.

Daga Ashura zuwa bayyanar Imam

Da yake magana kan dangantakar Ashura da Mahdawiyya, Hujjatul Islam Nasouri ya ce ba zai yiwu mutum ya ce shi mabiyin Imam Husaini (A.S) ne ba tare da la’akari da matsayinsa ga Imamin Zamani(A.F) ba.

Ya bayyana cewa, duk da cewa ya kamata musulmi ya koyi darussa daga tafarkin dukkan Imamai, ma’aunin gaskiya a zamaninmu shi ne yadda mutum yake mu’amala da Imamin Zamanida kuma yadda yake fuskantar zalunci da abubuwan da suka saba wa manufofin Ahlul-Baiti (A.S).

Ya ce la’antar maƙiyan Ahlul-Baiti (A.S) kaɗai bai isa ba; abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya duba irin gudunmawar da yake bayarwa wajen yaƙi da zalunci da kuma tsayawa kan tafarkin Imam Husaini (A.S).

Ya ƙara da cewa akwai alaƙa mai zurfi tsakanin juyin Imam Husaini (A.S) da tashin Imamin Zamani(A.F). A cewar ruwayoyin da aka ambata, lokacin bayyanar Imamin Zamani zai ci gaba da tafarkin kakansa Imam Husaini (A.S), yayin da taken mataimakansa zai kasance “Ya Litharatil Husaini”, wato masu neman ramuwar jinin Husaini.

Ya ce wannan yana nuna cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin al’adar Ashura da tashin duniya baki ɗaya na Imamin Zamani.

A ƙarshe, ya jaddada cewa idan mabiya Ahlul-Baiti (A.S) suka ɗauki darussan Ashura na tsayin daka, gyara da gwagwarmaya, sannan suka haɗa su da al’adar jira da samar da yanayin bayyanar Imam, za su iya taimakawa wajen gina al’umma mai tafiya kan gyara da aiwatar da koyarwar Ahlul-Baiti (A.S).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha